Immigration za ta fara bayar da Visa a cikin awa 48 | isyaku.com

Hukumar kula da shiga da fice ta kasa NIS ta fito da sabuwar tsari na bayar da VISA a cikin awa 48 bayan an kammala cika takardu ta sabuwar tsarin amfani da yanar gizo.

Babban jami'in hukumar ta kasa Muhammad Babande ya shaida wa manema labarai haka jiya a Abuja bayan kammala taro na kwana biyu da kuma gabatar da littafi akan sanin makaman aiki da kwarewa ta hanyar cima ka'idodin shugaban kasa akan sabon tsarin aikin hukumar shige da fice ta Najeriya wanda Ministan cikin gida Gen.AB Dambazau ya sami halarta.

Babande ya ce "matsawar mutum ya cika gurbi da  ka'idan abin da hukumarsa take bukata a cikin awa 48 zasu tuntube shi ta email kuma ka'idodin suna nan bayane a shafin yanar gizo na hukumar".

A nashi jawabi Gen.Dambazau ya jinjina wa hukumar ta shige da fice akan nassarori da ta samu wajen tafiyar da sabon tsarin shugaban kasa akan tafiyar da aikin na hukumar ya kuma ce zai tabbatar da cewa dukkanin hukumomi da ke karkashin ma'aikatarsa ta cikin gida sun cimma ka'idar shugaban kasa kan tafiyar da ayyukan su.@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.
Immigration za ta fara bayar da Visa a cikin awa 48 | isyaku.com Immigration za ta fara bayar da Visa a cikin awa 48 | isyaku.com Reviewed by on June 21, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.