Gwarawa sanye da Bente sun yi zanga zanga a Abuja | isyaku.com

Rahotanni da ke fitowa daga birnin tarayya Abuja sun nuna cewa da safiyar yau wasu al'umman Gbagi wanda aka fi sani da Gwari sun mamaye kofar shiga ginin Majalsar wakilai ta tarayya a Abuja sanye da shiga irin ta gargajiya inda suke sanye da bente,wasu kuma suna rike da kwari da baka a bisa tsarin al'adar Gwari.


Sahara Reporters ta ruwaito cewa Gwarawan suna nuna rashin jindadin su ne a kan abinda suka kira tauyesu da mahukunta ke yi a cikin yankin nasu na Abuja.

Masu zanga zangar sun ce zasu ba mazauna Abuja wa'adin zama a cikin ta matsawar hukumomi basu kula da bukatun su ba.@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

Hoto: Sahara Reporters
Gwarawa sanye da Bente sun yi zanga zanga a Abuja | isyaku.com Gwarawa sanye da Bente sun yi zanga zanga a Abuja | isyaku.com Reviewed by on June 13, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.