• Labaran yau

  June 14, 2017

  Gwamnatin tarayya ta gargadi masu yin kalaman tashin hankali | isyaku.com

  Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya ce gwamnatin tarayya za ta hukunta duk wani mutum ko kungiya dake yin wasu abubuwa da ka iya haddasa tashin-tashina a tsakanin al’umma.

  Osinbajo, ya yi gargadin ne a lokacin da yake ganawa da wasu shugabannin arewacin Najeriya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

  Wannan ya biyo bayan kira da wata kungiyar matasan arewacin Najeriya ta yin a cewa dukkanin ‘yan Kabilar Igbo su, bar yankin Arewa kafin ranar 1 ga watan Oktoba.

  Ya ce ya zama wajibi gwamatin tarayya ta rika maida hankali akan duk wasu kananan abubuwa da suka taso kamar haka, dan idan an san farkon abu, ba a san karshensa ba.

  Osinbajo, ya kara da cewa gwamnatin tarayya ba zata lamunci duk wani abu da ka iya barazana ga zaman lafiya a Najeriya ba, domin burin gwamnatin tarayya shine a samu zaman lafiya mai dorewa.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.

  Daga shafin Liberty
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamnatin tarayya ta gargadi masu yin kalaman tashin hankali | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama