• Labaran yau

  June 06, 2017

  Ganduje yayi sulhu tsakanin Abdulmumin da Majalisar Wakilai | isyaku.com

  Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yana wani yunkuri na sasantawa tsakanin dan Majalisan Wakilai na Najeriya da aka dakatar Abdulmumin Jibrin da kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da wasu masu mukamai a Majalisar.

  Bayanai sun nuna cewa Ganduje ya riga ya tattauna da Yakubu Dogara da wadanda zancen ya shafa kuma akwai yiwuwar za'a dage kangi da aka sanya wa Abdulmumin akan ladabtarwa.

  Majalisar Wakilai ta dakatar da Abdulmumin ne har tsawon kwanaki 180 na zaman  Majalisa bayan ya fallasa wata badakala a cikin kasafin kudi a Majalisar.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com


  Hoto: Leadership
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ganduje yayi sulhu tsakanin Abdulmumin da Majalisar Wakilai | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama