• Labaran yau

  June 13, 2017

  Fina-Finan Kannywood Guda 7 Da Zasu Fito Da Karamar Sallah | isyaku.com

  Manya manyan furodusosin masana’antar shirya fina finai ta Kannywood sun shirya fito da wasu daga cikin fina finan da aka dade ana tsumayi a lokacin shagulgulan sallah karama.

  Rahama Sadau za ta fitar da fim din ta mai suna Rariya wanda Yasin Auwal ya bada umarni a ranar 26 ga watan nan.

  Fim din Ali Nuhu Mansoor shi ma ana tsammanin zai fito a daidai lokacin da ake bukukuwan Sallar, haka zalika na Abubakar Mai Shadda Kanwar Duba rudu, wanda Ali Nuhu da Rahama Sadau suka fito a matsayin ya da kanwa.

  Sai kuma fin din Zaharaddeen Sani Abu Hassan wanda ya bada labarin tabargazar da wata kungiyar ta’addanci ta yi a gari kafin a karshe sojoji su murkushe ta.

  Sauran da ake tsammani za su fito a lokacin sun hada da BintotoSultana da Munaqisa
  An dai dakatar da fitowar fina finan saboda zagayowar watan Ramadan.

  Wannan shi ne karon farko a masana’antar da za a haska manyan fina finai irin wadannan a lokaci daya a sinima.



  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

  Daga  shafin Al'ummata
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Fina-Finan Kannywood Guda 7 Da Zasu Fito Da Karamar Sallah | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama