Dan ta'adda ya taka Musulmai da mota a yayin fito wa daga Sallar Tarawih a Landan | isyaku.com

A Landan babban birnin kasar Birtaniya an gano mutumin da ya bi ta kan Musulmi da ke fito wa daga Masallaci bayan gabatar da Sallar Tarawih.

Dan ta'addar mai suna Darren Osborne ne ya kai harin na ta'addanci da nuna kyamar Musulunci wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 1.

An bayyana cewa, dan ta'addar na da shekaru 40 kuma yana da yara 4.
Osborne ya bi ta kan mutanen da suke fito wa daga Masallaci bayan Sallar Tarawih inda ya jikkata mutane 9.

Shaidun gani da ido sun ce, kafin ya taka mutanen dan ta'addar ya ihu tare da cewa, zai kashe Musulmai.
Jama'ar da ke kusa da inda lamarin ya faru ne suka cafke dan ta'addar.

A gefe guda Turkiyya ta la'anci wannan hari na ta'addanci da nuna kyama ga Musulunci.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta fitar ta ce, suna la'antar harin da aka kai wa Musulmai a wurin shakata wa na Finsburyinda aka jikkata mutane da dama.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.


Daga shafin TRT
Dan ta'adda ya taka Musulmai da mota a yayin fito wa daga Sallar Tarawih a Landan | isyaku.com Dan ta'adda ya taka Musulmai da mota a yayin fito wa daga Sallar Tarawih a Landan | isyaku.com Reviewed by Isyaku Garba on June 20, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

Powered by Blogger.