Birnin kebbi: NSCDC ta damke barayin AC da suka addabi mazaura Dakingari kwatas

Rundunar tsaro ta NSCDC ta jihar kebbi tayi nassarar kama wasu matasa biyu da suka shahara wajen satan na'urar sanyaya daki watau AC a rukunin gidaje na Dakingari (Dakingari quarters) da ke kan hanyar Kalgo a jihar Kebbi.

Kwamandan rundunar da ke kula da gundumar Birnin kebbi CS Ibrahim Usman ya jagoranci jami'an rundunar wajen binciken farko a bisa rahotun fari wanda hakan ya haifar da samun nassara cikin gaggawa da sauki wajen damke wasu matasa biyu wanda yanzu haka suke taimakawa jami'an rundunar wajen bincike akan lamarin.

Bayanai sun nuna cewa matasan sun shahara wajen satan na'urar AC wanda ta hakan suka addabi jama'ar unguwar ta rukunin gidajen na  Sa'idu.Wani magidanci da ke zaune a rukunin gidajen na Sa'idu wanda bayason a bayyana sunansa ya shaida mana cewa yayi farinciki da jami'an na NSCDC suka yi nassarar damke wadannan yara da suka addabe su a unguwar.

Ofishin hukumar ta NSCDC ya cika makil daga wajen harabar ginin a yayin da jama'a suka yi cincirindo a bakin Ofishin sakamakon shigowa da barayin da akayi a cikin Ofishin.Bayan gudanar da bincike an garzaya da masu laifin zuwa babban hedikwatar hukumar a garin Birnin kebbi.An mika masu laifin a sashen binciken laifuka da leken asiri na hukumar inda ake ci gaba da bincike akan lamarin.

Kawo yanzu dai yunkurimu na muji ta bakin mai magana da yawun hukumar sashen hulda da jama'a kan lamarin yaci tura,haka kuma ba jami'in da yayi magana da mu akan lamarin kawo yanzu da muka rubuto wannan labarin.



 @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN