• Labaran yau

  June 09, 2017

  Bam da aka boye a laida yayi sanadin mutuwar yara 2 | isyaku.com

  Wasu yara guda biyu sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wani abu da ake kyautata zaton cewa bam ne da aka saka a cikin wata laida a karamar hukumar Hong da ke cikin jihar Adamawa ranar Alhamis da Magariba misalin karfe 7:00 a yayin da ake kokarin budin baki na watan Ramadan.

  Rahotanni sun nuna cewa wani mutum ne ya tuka wata mota zuwa inda wasu yara ke wasa sai ya mika masu laidar da ba'asan me yake kumshe a ciki ba kuma ya bukaci cewa sukai sakon kudi ne wa mahaifinsu wanda daga bisani bayan mai motar starlet din ya bar wajen sai aka sami fashewar abinda ke cikin laidar yayin da yaran ke kan hanyar su ta zuwa gida saboda su ba mahaifin su laidar kuma nan take ya haddasa mutuwar yaran guda biyu.Yayin da wasu masu wucewa a kusa da wajen suka sami munanan raunukka.

  Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Adamawa ya tabbatar da aukuwar lamarin,izuwa yanzu dai ba wanda ya dauki alhakin kai wannan harin.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Bam da aka boye a laida yayi sanadin mutuwar yara 2 | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama