• Labaran yau

  June 05, 2017

  APDA, wata sabuwar jam'iyar siyasa a Najeriya | isyaku.com

  An kirkiro wata sabuwar jam'iyyar siyasa a Najeriya da aka kira APDA (all peoples democratic alliance) wanda wani babban jimi'i a jam'iyar PDP Chief Raymond Dokpes da tsohon shugaban jam'iyar kwadago Dan Nwanyawu suka sami halartar taron jam'iyar da aka gudanar a Reiz Continental Hotel a birnin Abuja ranar Litinin.

  Wasu 'yan siyasa da suka halarci taron sun hada da Mahe Dange mataimakin Chiyaman na Arewacin Najeriya,Fijabi Adebayo mataimakin Chiyaman na kasa yankin kudu da Shittu Muhammed Chiyaman na kasa.

  Sai dai wani jigo a sabuwar jam'iyar Mr Nwanyawu ya musanta cewa PDP tana da hannu a kafa sabuwar jam'iyar saboda ta yi hadaka wajen kawar da jam'iyar APC mai mulki daga Gwamnati a zaben 2019.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

  Hoto: Sahara Reporters
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: APDA, wata sabuwar jam'iyar siyasa a Najeriya | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama