• Labaran yau

  June 06, 2017

  An gano Duniya da ta fi kowacce zafi a tsakanin Duniyoyi | isyaku.com

  An gano duniya mafi zafi a tsakanin duniyoyi wadda ke da nisan tafiyar haske ta shekara 650 kuma darajar zafinta ya kai dubu 4,300.


  Sakamakon binciken da aka buga a mujallar "Nature" na nuna cewa, duniyar na kama da duniyar Jupiter kuma an ba ta sunan "KELT-9b" kuma tana kammala zagayenta a kwana 1.5 na duniya. Sabuwar mai zafi ta ninka Jupiter girma sau 2.8.

  An gano KELT a yayin binciken da aka yi  Cibiyar Hangen Nesa ta Winer da kudu maso-gabashin Arizona, kuma ta ninka rana girma da zafi sau 2.  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

  Daga shafin TRT
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An gano Duniya da ta fi kowacce zafi a tsakanin Duniyoyi | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama