Aisha Buhari: Shugaba Buhari na samun sauki sosai


Uwargidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta ce mijinta na murmurewa sosai daga jinyar da yake yi a kasar Ingila. Tana magana ne a safiyar Talata bayan da ta dawo daga London, inda ta kai masa ziyarar mako guda.

Ta ce shugaban ya godewa 'yan kasar kan addu'o'in da suke yi masa da kuma goyon bayan da suke bai wa Mukaddashinsa Yemi Osinbajo.

Shugaba Buhari dai ya koma London ne a karo na biyu cikin wanann shekarar a ranar 7 ga watan Mayu, domin likitoci su sake duba lafiyarsa

Sai dai rashin lafiyar shugaban tana janyo ce-ce-ku-ce sosai a kasar, inda wasu ke ganin kamata ya yi shugaban ya yi murabus ya fuskanci kula da lafiyarsa.

Amma wasu kuwa suna ganin tun da ya mika ragamar shugabanci a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, to babu wani abin damuwa.

Har yanzu dai ba a san takamaimai cutar da ke damun Shugaba Buhari ba.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com


Daga BBC
Aisha Buhari: Shugaba Buhari na samun sauki sosai Aisha Buhari: Shugaba Buhari na samun sauki sosai Reviewed by on June 06, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.