• Labaran yau

  May 26, 2017

  Yunkurin juyin mulki: Sojin Najeriya sun yi raddi | isyaku.com

  Rundunar Sojin Nijeriya ta musanta rade-radin yunkurin juyin mulkin da wasu ke cewa an yi, inda ta ce sojojin Nijeriya ba su da niyar yi wa mulkin Dimokaradiya karan-tsaye.

  A wani taron manema labarai, Kakakin rundunar sojin Nijeriya Burgediya Janar Sani Usman Kukasheka, ya ce sojojin Nijeriya masu biyayya ne ga dokokin kasa da su ka shimfida mulkin dimokaradiya.

  Ya ce Sojojin Nijeriya sun ta’allaka ne ga yin biyayya ga shugaban kasa, da kuma kwamandan sojoji da tsarin mulkin kasa.

  Rundunar dai, ta bukaci ‘yan Nijeriya su kwantar da hankalin su, domin babu batun karbar mulki ta hanyar karfi.

  Janar Kuka-sheka, ya ce ana gudanar da bincike a kan yadda wasu rahotanni su ka ce ana zawarcin wasu sojoji domin juyin mulkin.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


  Wannan labarin ya fara bayyana a shafin Liberty.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yunkurin juyin mulki: Sojin Najeriya sun yi raddi | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama