'Yan sanda sun gurfanar da Sule Lamido gaban Kotu

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido a wata Kotu a Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Sule Lamido ya fada hannun 'yan sanda bayan Gwamnatin jihar Jigawa ta yi koke akan cewa yayi kalamai da ke iya tunzura jama'a.

Alkalin kotu Muhammad Lamin ya bayar da umarni acigaba da tsare tsohon Gwamnan duk da yake Lauyoyin Lamido sun bukaci a bayar da shi beli.

Ana tuhumar Lamido ne da laifuka hudu da suka jibanci ingiza Jama’a, bata sunan gwamna mai ci da kuma barazana ga zaman lafiya.

 Sai dai gwamnan ya musanta wadannan zarge zarge.

An dage sauraron karar zuwa ranar Alhamis mai zuwa.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
'Yan sanda sun gurfanar da Sule Lamido gaban Kotu 'Yan sanda sun gurfanar da Sule Lamido gaban Kotu Reviewed by on May 02, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.