Ya kashe ta domin ta ki ta koma soyayya da shi | isyaku.com

Wani mutum ya sassare wata mata guntu guntu a Labone da ke kasar Ghana,rahotanni sun nuna cewa mutumin wanda tsohon saurayin matar ne ya fusata ne a bisa dalilin cewa matar tayi yaji kuma ta kwashe kayakin ta ta koma wajen 'yar uwarta.Bayan ya lallasheta domin ta dawo wajensa ita kuma ta ki ta yarda sai ya fusata inda yaje ya samo adda kuma ya sassareta.

Majiyar mu ta shaida mana cewa matar ta kaurace wa mutumin ne a bisa dalilin cewa yana gana mata azaba ta hanyar duka.

Makwabata ne suka lura da abinda ya faru inda suka kai wa matar dauki ta hanyar daukanta su kaita Asibiti inda daga bisani ta mutu.

Tuni dai mutumin ya fada hannun jami'an tsaro a kasar ta Ghana.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
Ya kashe ta domin ta ki ta koma soyayya da shi | isyaku.com Ya kashe ta domin ta ki ta koma soyayya da shi | isyaku.com Reviewed by on May 17, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.