May 11, 2017

Wasikar Buhari: Muhawwara tsakanin 'yan majalisan Dattawa

Sai dai karanta wasikar ke da wuya muhawara ta barke tsakanin ‘yan majalisar, sakamakon korafin da wasu su ka yi a kan rashin bayyana Farfesa Yemi Osinbajo da Buharin yi a matsayin mukaddashin shugaban kasa a fayyace ba.

A cikin wasikar dai, shugaba Muhammadu Buhari ya ce babu kayyadajjen lokacin da zai dawo, dan haka mataimakin sa Farfesa Osinbajo zai cigaba da kula da al’amuran gwamnati, kamar yadda sashe na 145 a kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bada dama.

Al’amarin dai, ya janyo ka-ce-na-ce tsakanin wadanda ke ganin ya kamata shugaba Buhari ya ambaci Farfesa Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasa a fayyace.

Sai dai masu sharhi a kan al’amurran yau da kullum sun ce, kalamann da shugaba Buhari ya yi amfani da sun a nuna cewa, mataimakin sa ne zai cigaba da jagorancin shugabancin Nijeriya har zuwa lokacin da ya dawo.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


Wannan labarin ya fara bayyana a libertytvradio.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: Wasikar Buhari: Muhawwara tsakanin 'yan majalisan Dattawa Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama