Wanda ya kashe budurwarsa: "Hukuma tayi yadda ta ga dama da ni,banyi nadama ba" | isyaku.com

Mutumin da ya sassare budurwasa kuma lamarin da ya haddasa mutuwar matar a Asibiti a kasar Ghana ya shida wa 'yan sanda cewa shifa bai yi nadama ba kuma duk yadda 'yan sanda zasu yi da shi sun dade basu yi ba.Rex Kpanor dan shekara 29 kuma mai aikin shara a cibiyar Cardio Thoracic a Asibitin koyarwa na Korle-Bu da ke kasar Ghana ya sassare budurwar shi ne guntu guntu bayan wata zafaffar cacan baki a tsakanin su.

Majiyar mu ta labarta mana cewa wannan bayanin ya fito ne daga bakin kwamandan 'yan sanda na gundumar La Korle-Bu inda yace mutumin da aka kama a bisa zargin aikata wannan laifi bai nuna alamar da na sani ba ko abin ya dame shi.

Idan baku manta ba jiya ISYAKU.COM ya ruwaito labarin yadda lamarin ya faru kafin Rex Kpanor ya aikata kisan.Karanta labarin a nan


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
Wanda ya kashe budurwarsa: "Hukuma tayi yadda ta ga dama da ni,banyi nadama ba" | isyaku.com Wanda ya kashe budurwarsa: "Hukuma tayi yadda ta ga dama da ni,banyi nadama ba" | isyaku.com Reviewed by on May 18, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.