Taron matan IPOB: Matan Inyamirai sun tube domin nuna adawa da kutsen Sojoji | isyaku.com

Wasu mata na al'umman Abiriba a karamar hukumar Ohafia da ke jihar Abia sun tube domin su nuna rashin amincewar su da yadda Sojoji suka koresu daga wajen da suke yin wani taro.Matan dai magoya bayan kungiyar nan ce ta Inyamirai masu ra'ayin ballewa daga Najeriya IPOB.

Bayanai sun nuna cewa matan suna cikin gudanar da wani taro sai Sojoji suka isa gurin inda suka kore su.Daga bisani matan sun je suka tube sai suka dawo  wajen sanye da rigar nono da fatari ko buje wasu kuma sanye da gajeren wando.

Wannan irin lamarin na rashin kunya da taurin kai daga mata dai ba inda akeyinshi a Duniya face kudancin kasar Najeriya musamman yankin Inyamirai.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
Taron matan IPOB: Matan Inyamirai sun tube domin nuna adawa da kutsen Sojoji | isyaku.com Taron matan IPOB: Matan Inyamirai sun tube domin nuna adawa da kutsen Sojoji | isyaku.com Reviewed by on May 19, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.