Tanzania ta kori mutane dubu 10 daga aiki

Fararen hula dubu 10 ne shugaban kasar Tanzania ya kora daga aiki domin basu da ingantacen satifikate.
A ranar juma’ar da ta gabata ne shugaban kasar Tanzania John Magafuli ya kori fararen hula dubu 10 ciki harda manyan ma’aikata akan cewa basu ingantacen satifikate dake nuna cewa sun yi kamala karatun jami’a.
Korar aiki ya biyo baya ne bayan an go cewa kasar na rashin akalla dalar Amurka miliyan 10 a kowanne wata wanda ake anfani da shi domin biyan mutane 19,708 da ba a san ko su waye ba.

A cikin sanarwar da shugaban yayi ya ce, “yanzu haka na kori wadanda ke anfani da satifikate na karya da kuma wadanda ke anfani da satifikate din mutane domin su anshi albashi. Daga baya kuma zan gurfanar dasu a gaban kotu.”

Da yake bayani a gidan telebijin kasar a Dodoma, Magufuli ya ce za a gudanar da bincike akan albashin fararen hula dubu 1 da 538 da aka jinkirta.

A halin yanzu ana sa ran cewa gwamnatin zata dauki mutane dubu 60 aiki a tsakanin shekarar 2017-2018.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

 Tanzania ta kori mutane dubu 10 daga aiki ya fara bayyana ne a TRT

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN