Akalla mutane 50 sun mutu a wani mummunar hatsarin mota da ya auku a jihar Kebbi.Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya auku ne tsakanin Tsamiya da Bagudo kuma wadanda hatsarin ya rutsa da su galibi 'yan kauyen Tsamiya ne wandanda ke kan hanyar zuwa garin Lagos don kasuwanci.
Tsoho Gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa yace bai goyi bayan bincike da ake yiwa Mai Martaba Sarkin Kano ba.Wannan ya biyo bayan zargi da hukumomi keyi masa da sanya kansa a harkokin siyasa da aikata ba dai dai ba a Masarautar ta Kano.
Gwamnatin tarayya tace 'yan boko haram guda hudu ne ta sako domin ta ceto 'yan matan Chibok 82.
Jam'iyar PDP ta mayar da martani akan kalaman da Bola Ahmed Tinibu yayi cewa PDP bazata ci koda karamar hukuma daya ba a zaben kananan hukumomi da ake shirin yi a jihar ta Lagos.
Kungiyar kwadago ta kasa tayi barazanar shiga yajin aiki idan Gwamnati batayi komai ba akan albashin ma'aikata.
Cutar Ebola ta sake bulla a jamhuriyar Congo.
Dattawan Arewa sun jinjina wa shugaba Buhari akan bin doka ta hanyar damka amanar kasar nan ga mataimakin shi Yemi Osinbajo.
Wata babban Kotu a jihar Benin ta garkame wani jami'in zabe a bisa zargin almundahana
Haka kuma babban Kotu da ke Abuja ta bayar da belin tsohon Ministan birnin tarayya Bala Muhammed.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb

Tags:
LABARI