• Labaran yau

  May 31, 2017

  Sojoji da 'Yan sanda sun tafka fada a Calabar | isyaku.com

  Rahotanni daga birnin Calabar na jihar Cross River na cewa an tafka wani fada tsakanin 'yan sanda da sojojin ruwan Najeriya, inda ake tunanun an yi asarar rayuka da wasu da dama kuma sun jikkata.

  Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da  faruwar lamarin, inda har ta wallafa hotunan barnar da ta ce sojojin sun yi a ofishin 'yan sandan.

  Amma rundunar ba ta yi karin bayani kan asarar rayuka ko jikkata ba.

  Wasu rahotanni sun ce rikicin ya fara ne a yayin da wani dan sanda ya yi kokarin tsayar da motar sojojin, wadda ta ki bin umarnin danjar bayar da hannu.

  Fadan ya yi kamari ne yayin da wasu manyan jami'ai suka yi kokarin sasantawa, amma daga bisani sai al'amura suka rincabe.

  Kafar yada labarai ta Premium Times ta ruwaito cewa wani ganau ya shaida mata cewa daga nan sai sojojin suka shiga cikin ofishin 'yan sandan na Akim inda suka fara harbe-harbe suka kuma kona ofishin.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com  Wannan labarin ya fara bayyana a shafin BBC
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sojoji da 'Yan sanda sun tafka fada a Calabar | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama