Kwamandan rundunar sa kai na tsaro da aka fi sani da suna
Vigilante group of Nigeria reshen jihar Kebbi Kwamanda Muhammed Lawal Augie
wanda bangaren su ne Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da sahihancin su ya yi
bayani akan matsalolin da rundunar shi ta Vigilante take fuskanta a wani
tattaunawa da ISYAKU.COM yayi da shi a hedikwatar rundunar da ke fuskantar
babban kasuwar Birnin kebbi.
Kwamanda Lawal Augie ya shaida mana cewa zamani ya canza
hakama marasa gaskiya basa tafiya hannu sake suna tafiya da bindigogi irin na
zamani amma duk da haka 'yan Vigilante suna tare da Allah kuma kundin tsarin aikin su ya yarda
da su dauki bindigogi kirar gargajiya,saboda haka ya kamata Gwamnati ta taimaka
ma rundunar domin a sami wadatattun irin wadannan bindigogin ga jami’an
rundunarsa a fadin jihar Kebbi.Kowace karamar hukuma ta mallaki nata kana Hedikwata ya
zama tana da nata don tukarar kalubalen tsaro.
Augie ya kara da cewa a horo da suka samu daga rundunar sojan
Najeriya da hukumar ‘yan sanda ta Najeriya jami’i zai iya zama da bindiga da
harsasai har ya shiga aikin tsaro yayi ritaya bai harba ko kwara daya ba domin
harbi yana tafiya ne tare da doka da oda,illa ana rike bindigar ne domin kariya
ba wai mutum yayi amfani das hi ba a bisa lissafin kansa."Rashin wadannan
makaman yana daya daga cikin matsalolin mu,idan aka bamu bindigogin a bisa
horarwa da muka samu bazamu je mu harbi wadanda bai kamata ba".
Bincike da ISYAKU.COM ya yi ya nuna cewa ofishin Vigilante
na jiha baya da kaso na kowane wata a zaman tallafi ga rundunar daga Gwamnatin
jiha,amma ofishin kan sami tallafi idan da wani bukata na tsaro da ake bukatar
Vigilante domin su taimaka wa sauran jami’an tsaro wajen bayar da kariya ko
tsaro.
Kwamanda Lawal Augie ya roki Gwamnatin jihar Kebbi akan ta
kara taimaka ma rundunarsa da motoci koda lalatattu ne wadanda aka karba daga ‘yan
sanda sai a gyara a basu su zasu hakura dasu wajen tafiyar da aikin su.Kwamandan
ya kuma bada misalin wani barawo da suka kama wanda ya shahara wajen satan
injimin ban ruwa na noman rani bayan bayani da suka yi da shi ya nuna cewa ya
saci injin 18 a garin Argungu,amma da suka tsananta bincike ala tilas sauran
injin 17 suka fito bayan 18 na farko,ya kara da cewa wannan ai zagon kasa ne ga
shirin Gwamnati na inganta aikin noma musamman noman rani.
Kwamandan ya shaida mana cewa rundunasa tana da mutum 8000 a
fadin jihar Kebbi,amma mutum 1400 ne ‘yan sanda suka horar da su,yayin da mutum
1060 kuma Sojoji ne suka horar da su "bayan mun sami horon mukan dawo mu horar da jami’an mu abin da muka
koya".Kwamadan ya kara rokon Gwamnati akan ta taimaka ma rundunarsa da na’urorin
sadarwa domin saukaka tafiyar da aiki ta hanyar sama masu radiyon ova-ova da
sauransu.
Yayin da ISYAKU.COM ya tuntube shi akan zargi da wasu ke yi
wa jami’ansa akan cewa sukan yi abin da wasu ke ganin cewa shiga sharo ba shanu
ne akan wasu lamura da ba hurumin rundunar Vigilante ba sai Kwamanda Lawal
Augie ya shaida mana cewa ba shiga sharo ba shanu bane,yace doka ta ba rundunarsa
dama tayi sulhu a dukkan lamurra da zai kai ga samun zaman lafiya a cikin al’umma
da kasa baki daya.Ya shaida mana cewa ai kara da da ake kawowa jama’a ne ke
kawowa ba wai Vigilante ne ke yin awon gaban kanta ba.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
Kana sha'awar ka taimaka mana da labarai daga garin da kake domin mu wallafa a ISYAKU.COM? Ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com ko ka aiko sakon SMS kawai zuwa 08062543120
Kana sha'awar ka taimaka mana da labarai daga garin da kake domin mu wallafa a ISYAKU.COM? Ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com ko ka aiko sakon SMS kawai zuwa 08062543120
Tags:
SHARHI