• Labaran yau

  May 22, 2017

  Rundunar Sojin Najeriya ta fara kame-kamen wasu Sojoji | isyaku.com

  Rundunar Sojan Najeriya ta fara kame kamen wasu Sojoji a wani lamari da ake zargin cewa suna hulda da wasu 'yan siyasar kasar a bisa manufa da ya saba ka'idar tsarin aikin Soja

  Sashen ayyukan leken asiri na rundunar ya fara wani bincike na kwakwab akan wasu Sojoji da ake zargi da shiga harkokin siyasa.

  Shafin yanan gizo na naij.com ya ruwaito a kwanakin baya cewa ana zargin cewa wasu Sojoji na hulda da wasu 'yan siyasa a bisa manufa na yiwuwar juyin mulki.

  Shugaban rundunar Sojin kasa ta Najeriya Laftanan Janar Tukur Brutai ya gargadi Sojojin Najerya da cewa su kaurace wa shiga harkar siyasa domin duk wanda aka samu da hannu cikin wannan lamarin zai dandani kudarsa.

  Jaridar Punch ta ruwaito cewa an kama wasu daga cikin Sojojin da ake zargi da hannu cikin sha'anin juyin mulki amma hukumar ta Soja bata son jama'a su sani saboda kada a tayar da hankalin jama'a.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rundunar Sojin Najeriya ta fara kame-kamen wasu Sojoji | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama