Birnin kebbi: Mawaki Sadiq ya sami kyautar Naira Miliyan 1,mota da babur | isyaku.com

An gudanar da bikin tunawa da ranar da Najeriya ta koma mulkin Dimokaradiyya a 29/5/1999 a babban filin wasa da ke sakatariyar Haliru Abdu a cikin garin Birnin kebbi wanda ya sami halarcin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Baguda da Mataimakinsa Samaila Dabai Yombe da Sakataren Gwamnati Babale Umar da sauran mukarraban Gwamnati.

Cikin shagulgular da aka yi a wajen bikin ya hada da pareti da rundunar yansanda suka yi da sauran Ma'aikatan Gwamnati,da wakoki daga mawaka na jihar kebbi,wasan tauri da wasu Mawaka da aka gayyato daga jihar Kano da sauransu.

Mawaki Sadiq daga jihar Kano ya sami kyautar Naira Miliyan daya da mota,babur da kuma sauran daruruwan Naira.Haka zalika saura mawaka sun tashi da kyautar motoci da babura da daruruwan Naira.

A yayin da yake jawabin godiya a wajen taron,Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu yayi godiya ga manya da kanan jami'an tsaro a bisa gudunmawa da suke bayarwa wa Gwamnatinsa wajen tafiyar da harkokin Gwamnati da sauran manyan baki musamman 'yan Majalisa da Sarakuna.

Mai Martaba Sarkin Zuru ne ya sami halartar bikin yayin da sauran Sarakuna na jihar Kebbi suka aiko wakilansu saboda wasu dalilai da suka sha karfinsu.

Gwamna Atiku ya kuma yaba wa ma'aikata,manoma da saura jama'ar jihar Kebbi da suka bayar da hadin kai wa Gwamnatinsa da Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.Ya kuma gode wa 'yan jarida a bisa kokarin su wajen sanar da al'umman jihar Kebbi ta hanyar yada al'amurra,manufofi da ayyukan Gwamnati.

Gwamnan ya shaida wa jama'a cewa akwai shirin bayar da rance na N140,000 a manomi wanda Gwamnatin tarayya ta amince a bayar amma shirin zai fuskanci kyakkyawar tsari domin a kauce wa rashin biyan bashin a laokacin da ya kamata.



@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN