• Labaran yau

  May 17, 2017

  Rahotun karya: EFCC ta gurfanar da mutum 2 a gaban Kotu | isyaku.com

  Hukumar da ke yi wa masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC ta kama wasu mutane guda biyu bisa tuhumar su da baiwa hukumar labarai na karya wanda ya sa hukumar ta karbo takardar waranti inda ta caji gidajen wasu mutane biyu a Maiduguri.

  A ranar Talata 16 Mayu 2017 hukumar ta EFCC ta gabatar da Buhari Fannami da Bakura Abdullahi a gaban Mai shari'a M.T Abdullahi na babban Kotun tarayya da ke Maiduguri a bisa tuhar su da bayar da rahotu da bayanan karya ga hukumar karkashi shirin Gwamnatin tarayya da fallasa ko tsegunta wadanda suka saci kudaden jama'a.

  EFCC dai ta binciki gidan wani mutum Ba'a Lawan bayan ta samo waranti akan ta bincike gidan kuma daga bisani ba'a sami komai ba,alhali wadanda suka gurfanar gaban Kotun sun shaida wa hukumar cewa akwai kudade da yawa da aka bizine a gidan Ba'a Lawal.

  Mai shari'a M.T Abdullahi ya dage sauraron shara'ar zuwa ranar 7 da 8 na Yuli domin sauraro kuma ya bayar da umarni a tsare wadanda ake tuhumar a gidan Yari.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rahotun karya: EFCC ta gurfanar da mutum 2 a gaban Kotu | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama