Namadi Sambo yayi ganawar sirri da Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi ganawar sirri da tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Yayin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawar, Namadi Sambo ya ce ya kai Osinbajo ziyarar sada zumunta ne kawai ba wani al’amari na daban ba.

Ya ce ziyara makamanciyar wannan ba sabon abu ba ne, kamar dai yadda tsohon ubangidan sa Goodluck Jonathan ya sha kai wa shugaba Buhari ziyara a ofishin sa da ke Abuja.

Wannan dai ita ce ziyara ta biyu da Namadi Sambo ya kai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, tun bayan da aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2015.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Wannan labarin ya fara bayyana a shafin Liberty tvradio 
Namadi Sambo yayi ganawar sirri da Osinbajo Namadi Sambo yayi ganawar sirri da Osinbajo Reviewed by on May 12, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.