May 13, 2017

Mugunta: Wata Mata ta kulle yara 3 a wani daki da niyyar kashe su da yunwa

Wata mata wadda kishiya ce ga uwar wasu yara da ubansu ya auro ta kulle yaran su uku a cikin wani daki a gidan kuma babu abinci ko ruwan sha da niyyar cewa yaran su mutu da yunwa a cikin birnin Kano..

Majiyar mu ta labarta mana cewa hakan ya farune bayan uban yaran yayi balaguro,sai wannan matar ta aikata wannan aika-aikan.Babu cikakken bayani ko kwana nawane yaran suka yi a kulle.

Makwabta sun lura da abin da ke faruwa bayan yaran sunyi ta sheka ihu,tuni dai bala'in yunwa da kishin ruwa ya baiyana a jikin wadannan yaran bayin Allah kafin makwabta su cece su.

Bayanai sun nuna cewa an gabatar da matsalar gaban hukumomin tsaro a jihar ta Kano.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: Mugunta: Wata Mata ta kulle yara 3 a wani daki da niyyar kashe su da yunwa Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama