Me ya sa Buhari bai halarci taron majalisar ministoci ba?

Rahotanni daga fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ana cewa shugaban bai fito taron majalisar ministoci da aka saba yi duk ranar L...

Rahotanni daga fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ana cewa shugaban bai fito taron majalisar ministoci da aka saba yi duk ranar Laraba ba, wanda hakan ya zama karo na uku kenan a jere da bai halarta ba.

Abokin aikinmu Haruna Tangaza wanda ya halarci fadar shugaban kasar tun da safe, ya ce ba a ga alamar shugaban ba har zuwa lokacin da 'yan majalisar taron suka gama hallara.
Ya ce, mataimakin shugaban Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taro wanda aka fara da misalin karfe 11 na safiyar Larabar

 Dama dai ana ta rade-radin cewa lafiyar shugaba Buharin na cikin wani yanayi mara dadi, duk da cewa a ranar Talata an bayar da rahoton fitowar sa ofishinsa na cikin gida, inda har ya gana da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar biyu.

An yi wannan taro an gama ne tsakanin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da ministocin kasar.

Tun farkon fara taron shugaban bai bayyana ba kuma ba alamu na bayyanarsa, ba kamar karon farko da bai zo taron ba inda aka yi ta jiran zuwansa kafin daga bisani aka ce Mista Osinbajo ya ja ragamar taron.
A wannan karon kai tsaye aka fara taron da isar Mista Osinbajon.

Da yake kafofin yada labarai sun wallafa labarin rashin halartar shugaban tun kafin kammala taron, hakan tasa da fitowar su, ministan yada labarai na kasar Alhaji Lai Mohammed ya shaidawa manema labarai dalilin rashin halartar shugaban a wannan karo.

Mista Mohammed ya ce, shugaba Buharin bai fito ba ne saboda har yanzu yana bin shawarwarin da likitoci suka ba shi cewa ya ci gaba da hutawa a gida.

Lai ya ce rashin lafiyar shugaban ba ta kai yadda ake kururutawa a shafukan sada zumunta da muhawara ba.
An dai ci gaba da ce-ce-ku-ce a kasra kan halin da lafiyar shugaba Buharin ke ciki.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Me ya sa Buhari bai halarci taron majalisar ministoci ba? ya fara bayyana ne a shafin BBC Hausa

 

COMMENTS

Name

AL-AJABI,25,BIDIYO,1,BIRNIN-KEBBI,26,DUNIYA,23,FADAKARWA,23,FASAHA,3,HOTUNA,40,JAKAR MAGORI,18,LABARI,422,NISHADI,51,SANARWA,13,SHARHI,13,SIYASA,17,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Me ya sa Buhari bai halarci taron majalisar ministoci ba?
Me ya sa Buhari bai halarci taron majalisar ministoci ba?
https://2.bp.blogspot.com/-TTNuZ7kBffU/WQn7CRdtXPI/AAAAAAAAEbs/c0OoLqHS66MRfjIrTiJUKqQtkgRX8IhWgCLcB/s400/buharihealth.jpg
https://2.bp.blogspot.com/-TTNuZ7kBffU/WQn7CRdtXPI/AAAAAAAAEbs/c0OoLqHS66MRfjIrTiJUKqQtkgRX8IhWgCLcB/s72-c/buharihealth.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/05/me-ya-sa-buhari-bai-halarci-taron.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/05/me-ya-sa-buhari-bai-halarci-taron.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts KARANTA SAURAN LABARAI Karanta saura Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All KARANTA WADANNAN LABEL MAADANI BINCIKA GABADAYAN LABARAI Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy