Manoma shinkafa jihar Kebbi:Tattaki domin nuna adawa da shigowa da shinkafa | isyaku.com

Da safiyar yau Talata Manoma shinkafa na jihar Kebbi suka gudanar da wani tattaki na lumana daga randabawal na Rima a garin Birnin kebbi zuwa gidan Gwamnatin jihar kebbi rike da kwalaye da aka rubuta kalamai na rashin amincewa da shigowa da shinkafa a Najeriya.

Manoman suna zargin cewa wasu mutane a mataki na Gwamnatin tarayyar Najeriya suna cusa wa Gwamnatin tarayya ra'ayin cewa a shigo da shinkafa daga kasar waje zuwa Najeriya.

A yayin da ISYAKU.COM ya tuntubi shugaban sashen harkar noman shinkafa na jihar Kebbi Alh.Sahabi Augie ya shaida mana cewa suna gudanar da wannan jerin gwano ne domin su baiyana korafin su game da matsalar da ke shafuwar manoman shinkafa a jihar Kebbi.

Sahabi Augie ya kara da cewa bayan an tabbatar da ingancin shinkafa na jihar Kebbi kusan ko'ina a kasar nan sai kuma ga wasu da suke ganin wannan abin baiyi masu dadi ba ko kuma suna gani an toshe masu wata hanya ta samun kudi ta son kansu ba ta cin gaban kasa ba suna son su nemi Gwamnatin tarayya ta bayar da dama domin a dage kangin da aka sanya na shigowa da shinkafa daga kasashen waje.

Ya kuma kara da cewa idan hakan ya faru manoman shinkafa a jihar Kebbi zasu yi asara saboda bayan an gama girbe amfanin gona kuma aka dinga shigowa da shikafa daga kasar waje hakan zai haifar da matsala ta asara ga manoman shinkafa na gida.

Masu tattakin sun sami shiga cikin gidan Gwamnati cikin lumana inda Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu da Mataimakinsa Samaila Dabai Yombe da sauran manyan jami'an Gwamnati suka tarbe su.

A nashi jawabin,bayan ya karbi takardar koke da masu tattakin suka gabatar masa ta hannun Alh.Sahabi Augie Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya tabbatar masu da cewa zai kai korafin su zuwa ga Mukaddashin shugaban kasa Prof.Yemi Osinbajo domin neman ganin Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi nazari akan lamarin.

Gwamana Atiku Bagudu yayi bayani akan muhimmancin inganta shinkafar da ake nomawa a cikin Najeriya musamman a jihar Kebbi inda ya nuna cewa shinkafar jihar Kebbi ta fi ta kowace kasa a Duniya inganci.
Ya kuma yi bayani akan wani sabon tsari da za'a sake ba Manoma bashi domin noman shinkafa,amma ya ce wannan karon sharadin bashin zai fi na baya tsauri kadan saboda 'yan matsaloli da aka samu wajen biyan bashin da aka karba a baya.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

 
Kana sha'awar ka taimaka mana da labarai daga garin da kake domin mu wallafa a ISYAKU.COM? Ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com ko ka aiko sakon SMS kawai zuwa 08062543120



Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN