Labarai a takaice

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa dake binciken zargin kashe wasu kudade da suka kai Naira Biliyan shida ba bisa ka'idi ba da ake yiwa masarautar Kano a Njeriya ta jingine bincike da ta fara.
Hukumar sauraron koke-koken jama'a da yakar cin hanci da rashawa ta jingine binciken ne har illa ma sha'a.
Majalisar Dokokin jihar Kano ita ma ta kaddamar da binciken Masarautar ta Kano saboda zarge-zarge masu yawa da ake yiwa Majalisar Sarkin Kano


Mayakan Boko Haram din da gwamnatin Najeriya ta saka bayan kungiyar ta saki 'yan matan Chibok 82 sun ce ba za su yi sulhu da gwamnati ba suna masu cewa nan gaba kadan za su soma kai hare-hare a kasar.
Wani bidiyo da kungiyar ta fitar ranar ya nuna mayakan na Boko Haram hudu a cikin wani daji, inda daya daga cikinsu wanda ya bayyana kansa da suna Abu Darda ya sha ce ba za su taba yin sulhu da gwamnatin Najeriya ba.


Tsohon mai taimakawa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ta fannin hulda da jama’a Doyin Okupe, yace rashin sanin yakamata ne kira da wasu keyi cewa shugaba Muhammadu Buhari, yayi murabus domin jinya da ta same shi.Doyin Okupe wanda ya kasance baya marawa Buhari baya amma batun kira da yayi murabus abun takaici ne, a matsayinsa na wanda ya fito daga yankin kudu yace tundawowar dimokradiya 1999, kudu tayi mulki na tsawon shekaru goma sha hudu (14) inda arewa ta sami hudu (4) don haka yake da ra’ayin a 2019, mulkin ya sake zama a yankin arewa maso yamma.


Kwamitin harkokin addini na majalisar dattijan Pakistan ya amince da yi wa wata doka gyara, wacce za ta tanadi hukunci mai tsanani a kan duk wanda aka kama ya karya azumi a watan Ramadana dake tafe.
Dokar za ta tanadi cin tara mai yawa da kuma daurin wata uku a gidan kaso ga Musulmin da aka samu yana shan taba ko cin abinci a bainar jama'a a lokacin azumin Ramadana.


Wani ɗaurarre da ke jiran a zartar masa da hukuncin kisa a jihar Georgia ta Amurka ya nemi a yi masa haddi ta hanyar bindigewa kan hujjar cewa allurar mutuwar da ake yi, za ta yi masa ciwo matuƙa.
J W Ledford Jr yana shan magani saboda ciwon tsikokin jiki abin da lauyansa ya ce ka iya shafar zubin sinadaran ƙwaƙwalwa, ya kuma sanya shi "ciwon da bai saba ji ba"


Yayin da sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fara aiki, al'ummomin Afirka za su zura ido su ga yadda zai cika wasu alkawura da yayi wa nahiyar a lokacin da yake yakin neman zabe.
Macron mai sassaucin ra'ayi da ke goyon bayan haɗin kan Turai ya yi alƙawarin farfaɗo da tattalin arziƙin Faransa da yi wa tsohon tsarin siyasar ƙasar garambawul.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb



Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN