• Labaran yau

  May 21, 2017

  Kishi: Uwargida ta kwara ma mijin ta ruwan zafi har ya mutu | isyaku.com

  Wani mutum ya rasa ransa bayan matarsa ta kwarara masa tafasashshen ruwanzafi a yayin da yake barci a gidansa a makn da ya gabata a garin Kaduna.

  Majiyar mu ta labarta mana cewa an garzaya da mutumin zuwa wani Asibiti inda yayi jinya na wasu 'yan kwanaki amma daga bisa ya rasu.

  Bayanai sun nuna cewa dama uwargidan nashi ta gargade shi akan cewa kada ya kara wata matar a zaman kishiya,amma yayi biris da gargadin nata wanda ya kai ta ga aikata wannan danyen aikin.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kishi: Uwargida ta kwara ma mijin ta ruwan zafi har ya mutu | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama