• Labaran yau

  May 18, 2017

  Kisan 'Yar sanda: An kama wadanda suka kashe Sajen Helen

  Jami’in tsaro sun kama ‘yan ta’addan da su ka kashe dogarin mataimakin gwamnan jihar Enugu.

  An dai kama ‘yan ta’addan ne bayan wata musayar wuta da aka yi tsakanin su da jami’an ‘yan sanda, inda su ka yi nasarar kama wasu yayin da wasu su ka ranta a nakare.

  Yanzu haka dai, jami’an ‘yan sanda sun bada sanarwar cewa, jama’a su sanya idon a kan mutanen da shiga asibito domin neman magani, kuma da zarar an ga wanda ke dauke da raunin harbin bindiga a yi gaugawar sanar da su.

  Marigayiya Sajen Helen Sunday dai, ta cika ne a wani asibiti sakamakon harbin da ‘yan ta’addan su ka yi mata a makon da ya gabata.

  Barayin dai sun yi kokarin yi mata fashi amma ba su samu nasara ba, inda a karshe su ka yi mata ruwan harsashi sannan su ka kwashe mata wayoyi.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


  Wannan labarin ya fara baiyana a shafin Liberty .
   
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kisan 'Yar sanda: An kama wadanda suka kashe Sajen Helen Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama