• Labaran yau

  May 20, 2017

  Ka'oje: 'Yan sanda sun kama mai tone gawa domin yayi tsafi da sassan jikinta | isyaku.com

  Hukumar 'yan sanda ta jihar Kebbi ta kama wani mutum mai suna Danbaba Umar dan shekara 35 kuma uba ga yara 10 a bisa zargin kutsawa cikin Makabarta da dare da yunkurin tone gawa saboda dalilai na tsafi a garin Ka'oje a karamar hukumar Bagudo.

  Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kebbi Ibrahim Kabiru ya shaida wa manema labarai haka a jiya a garin Birnin kebbi.

  Bayanai sun nuna cewa wanda ake zargin ya shiga makabartar ne da misalin karfe 3:30 na dare saboda ya tone wata sabuwar gawa da niyyar ya sare kanta domin sha'anin tsafi. 

  Labari da muka samu daga wata majiya kuma ya nuna cewa wani Malami ne da ke zaune a garin Sokoto ya bukaci  Danbaba ya kawo kan dan adam domin yayi masa kudi ta hanyar tsafi.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ka'oje: 'Yan sanda sun kama mai tone gawa domin yayi tsafi da sassan jikinta | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama