• Labaran yau

  May 28, 2017

  Kebbi: Gwamnati ta fara feshin maganin tsuntsaye da jirgin sama | isyaku.com

  Gwamnatin jihar Kebbi ta fara feshin maganin tsunsaye da ke yin bairna ga amfanin gona ta hanyar amfani da jirgin sama.Tsunsayen da ake kira Quela birds sukan yi mummunar barna ga gonar shinkafa da sauran amfanin gona.

  A yayin da yake kaddamar da shirin a garin Tuga ,Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Dabai Yombe ya ce tsuntsayen sukan yi mummunar barna a duk lokacin da suka ziyarci gonaki musamman wadanda aka  shuka tsaba.

  Yombe ya kara da cewa Gwamnati ta bayar da mahimmanci ga aikin noma ta hanyar sa dogaro da kai ta aikin noma,haka zalika yace Gwamnati ta kashe Naira Miliyan 200 a kowane shekara wajen taimaka wa manoma a kori tsuntsayen daga gonaki ta hanyar feshin magani saboda manoma su tabbatar da samun wadataccen amfanin gona.  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi: Gwamnati ta fara feshin maganin tsuntsaye da jirgin sama | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama