Kebbi: Gwamnati ta biya N274.4.m kudin rijistan dalibai na manyan makarantu

Gwamnatin jihar Kebbi ta biya Naira Miliyan 274.4 kudin rajistan Dalibai 'yan asalin jihar Kebbi da ke karatu a makarantu da ke kasashen waje.

Sakataren watsa labarai na Gwamnatin jihar Kebbi Alh.Abubakar Dakingari ya shaida wa manema labarai a gidan Gwamnati ranar Lahadi.

Bayanai sun nuna cewa kudaden rijistan ya shafi dalibai da ke Makarantun da suka hada da Kwalejin ilimi da ke Kebbi,Sokoto,Dakin gari da kuma Zaria.Sai kuma Jami'oi da suka hada da Jami'ar Kano da Sokoto da kuma Makarantar kimiyya da ke Kaduna KADPOLY da makarantar Ilimi da ke Yauri.

Za'a kashe miliyan 28.4 a wasu ayyuka da suka wajaba a ma'aikatar ilima na jihar Kebbi .

Haka kuma Gwamnati ta saki Nairaa miliyan 56 domin kwashe shara a Sakaba da biyan kudaden da suka rataya a kan Gwamnati da kuma yin kwalbatoci a garin Maiyama.

Sa'annan Naira miliyan 15 za'a yi amfani da su wajen siyen motar sadarwa ta zamani a ma'aikatar sadarwa ta jihar Kebbi tare da biyan kudaden ayyuka da suka wajaba a ma'aikatar.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


Kebbi: Gwamnati ta biya N274.4.m kudin rijistan dalibai na manyan makarantu Kebbi: Gwamnati ta biya N274.4.m kudin rijistan dalibai na manyan makarantu Reviewed by on May 15, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.