Kebbi: Gwamnati ta bayar da tallafin Naira Miliyan 3 ga wadanda suka rasa muhalli a Ribah

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh.Samaila Dabai Yombe ya bayar da tallafin naira miliyan 3 wa wadanda suka rasa muhallin su sakamakon ruwan sama da aka yi a garin Ribah a karamar hukumar Danko/Wasagu da ke Masarautar Zuru.

Mataimakin Gwamnan ya baiwa wata mata da mijinta ya rasu Naira Miliyan daya bayan gidan da take ciki ya salwanta yayin da sauran wadanda abin ya shafa aka basu Naira Miliyan biyu,

Samaila Dabai Yombe ya umarci Kantoman karamar hukumar Danko/wasagu akan ya tsara sunayen wadanda lamarin ya shafa domin Gwamnati ta tsara yadda za'a taimaka masu,haka ma hukumar bayar da agaji na gaggawa ta Najeriya NEMA .


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
Kebbi: Gwamnati ta bayar da tallafin Naira Miliyan 3 ga wadanda suka rasa muhalli a Ribah Kebbi: Gwamnati ta bayar da tallafin Naira Miliyan 3 ga wadanda suka rasa muhalli a Ribah Reviewed by on May 09, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.