Kanwar Uwa ta maka wa dan shekara 10 dutsen guga mai tsananin zafi

Wata mata mai suna Mama Arafat wadda kanwa ce a uwar wani yaro mai suna Fawaz ta azabtar da yaron ta hanyar maka wa yaron dan shekara 10 dutsen guga mai tsananin zafi a kirjinsa a bisa zargin sata kamar yadda wata ma'abuciya amfani da shafin yanan gizo  ta ruwaito.

Bayani ya nuna cewa uwar yaron ta taho da shi ne daga jihar Osun kuma suna zaune a unguwar Na'ibawa a Kano.Bayanan sun kara da cewa yaron dai baya zuwa Makaranta ,babu jindadi balle annashuwa ko cikakken kulawa,hatta ma wani sa'ilin a waje yake kwana wanda hakan zai iya haifar da fargaban cewa kada ya fada hannun 'yan luwadi wanda zasu iya amfani da wannan damar su afka masa.


@isyakuweb   https://web.facebook.com/isyakuweb

Kanwar Uwa ta maka wa dan shekara 10 dutsen guga mai tsananin zafi Kanwar Uwa ta maka wa dan shekara 10 dutsen guga mai tsananin zafi Reviewed by on May 01, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.