• Labaran yau

  May 21, 2017

  Jita-Jitan canjin shugabanci: Britaniya ta gargadi Sojoji da 'yan siyasan Najeriya | isyaku.com

  Kasar Britaniya ta gargadi manyan hafsoshin Sojin Najeriya da ma sauran 'yan siyasa akan cewa kada su kuskura su yi tunanin shirya canjin shugabanci sakamakon rashin lafiyar shuga Muhammadu Buhari.

  Daily Post ta ruwaito cewa jakadan kasar Britaniya wadda ita ce tayi wa Najeriya mulkin mallaka  Mr. Paul Arkwright ya ce kasar Britaniya zata ci gaba da goyon bayan Gwamnatin dimokaradiyya a zaman tsarin Gwamnati karbabbiya.

  Jakadan ya kara da cewa duk wanda ke bukatar wani canji to tilas ne ya bi hanyar dimokaradiyya watau ta hanyar zaben kada kuri'a.

  Daily Post ta kara da cewa Mr.Arkwright ya mayar da martani ne game da bayanan da suka fito daga bakin shugaban rundunar Sojan kasa ta Najeriya Gen.Tukur Brutai cewa wasu 'yan siyasa suna tuntuban wasu Sojin kasan da zancen yiwuwar canjin shugabanci.

  Mr Arkwright yace " A 2015 an gudanar da zabe a Najeriya kuma shine Britaniya take bukatar gani anyi,saboda haka matsayin mu a fili yake cewa muna goyon bayan tsarin dimokaradiya idan ma har wani canji ake bukata a Najeriya".


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jita-Jitan canjin shugabanci: Britaniya ta gargadi Sojoji da 'yan siyasan Najeriya | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama