• Labaran yau

  May 28, 2017

  Huduba daga Limamin babban Masallacin jihar Kebbi (kaso na 2) | isyaku.com


  Ya yi maka baki, Ya sanya maka dandano don ka amfanu da dandano daban daban, ya sanya maka sha’awar abinci don Ya saukaka maka cin shi tare da dandano, Ya sanya maka jin kanshi mai dadi da Jan ra'ayi ga abinci da ke janka zuwa gare shi da ire-iren wadannan ni’imomi ba don wata dabara taka ba.

  Ya saukaka maka narke abincin, tun daga baki har cikin hanji da zuke ababen da jikinka ke bukata don samun karfi da lafiyaba tare da ka wahala ba, ba tare da an kallafa maka biya ba, ba tare da ka bukaci canja baki ko kayan ciki ba, yau da kullum ko mako mako ko wata wata ko shekara shekara kobayan shekaru, a'a duk tsawon rayuwa. 

  Haka ne game da amfani da sauran gabbbin jiki da ni'imomi da yawa daga ni'imomi da yawa da Allah Ya yi maka, sai dai kadan ne kake gode ma Allah bisa ga ni'imominsa masu daraja da tsada da Ya yi maka da iyalinka da mutane baki daya.


  Allah Ya saukake maka ka rayü kana mai nishadi lafiyayye ba da neman shawararka ba, ko don ka nemi hakan ba, Ya karfafa ka da karfin da ya dace da kai da lafiya.Ya azurta ka da kyawawan abubuwa na halal, Ya hore makahanyoyin rayuwa. Dukkan wadannan ababen ba wanda ka yi wa kanka daga cikinsu, sai dai ni'imar Ubangijinka kuma falalar Allah gare ka mai girma ce. Amma sai kana butulce maSa kana ta saba maSa, shin ba ka jin kunya.

  Allah Madaukaki Ya Ce:- "Shin su ke raba rahamar Ubangijin ka? Mu, muka raba (Harkokin) rayuwa a tsakanin su, a rayuwar duniya kuma muka daukaka sashensu saman sashe ga darajoji, don sashensu, su riki sashe ma'aikata küma rahamar Ubangijinka ta fi alheri fiye da abin dâ suke tarawa. Zukhruf. Kuma Ya Ce: "Kuma Mun sanya yini lokacin neman abinci" 31 Naba'u. Kuma Ya ce:- "Hakika Mun ba ku dama a cikin kasa kuma muka sanya maku hanyoyin rayuwa a cikinta, kadan ne kuke godewa, A'araf 10. 

  Kuma Ya Ce:- "Kuma Mun sanya maku hanyoyin rayuwa a cikinta, da wadanda ba ku ne ke arzurta su ba. Hijr 20,Ga ka nan Ya kai mutum kana munana amfani da wadannan ni'imomi masu yawa da damar da ka samu da ya wajaba ka yi  amfani da su ga da'ar Ubangijinka Mai girma, da gode maSa a kan ni'imominSa gare ka, sai ga ka nan kana tajan jiki da kasala ga yi maSa da'a da godiya. 

  Kai ga butulce ma ni'imominsa kafi nishadi, kafi dogewa ga barna, kafi lazimtar sabo. Kuma sau da yawa hakan ka kasancewa da sunan neman abinci da jin dadi, kana zaton kana shirya wa kanka aiheri ne, a dunlyarka da lahirarka? Me zal sa ka fifita duniya a kan lahira in ba wauta da batan basiraba.


  Yaya za ka yi rayuwa ingantatta, mai nasara a duniya kuma ka tsira a lahira, aihali ka mayar da kanka makaho bayan ka kasance mai gani? Game da haka ne Allah Madaukaki ke cèwa: "Wanda ya kasance makaho a cikin wannan (duniya), to shi a lahira mãkaho ne kuma ma bata ga hanya. Isra'i 72. Ya kuma Ce: "Duk wanda ya bijire daga ambato Na, to hakika yana da rayuwa mai kunci, kuma Mu tada shi ranar kiyamá makaho. 

  Ya Ce: Ya Ubangijina! Mi da ka tada ni makaho aihali na kasance mai gani. Sai Ya Ce: "Kamar haka ne ayoyinMu suka zo maka, sai ka  manta su, to kamar haka ne yau ake manta ka. Kamar haka ne Muka sakanta wa wanda ya yi airnubazzaranci, bai yi imani da ayoyin Ubangijinsa ba kuma azabar lahira ita ta fi tsanani da wanzuwa. Daha 123 - 127.


  Kana ta kunbura kana fadin rai da fandara, kana takama da hurahanci sai ka ce kai ka halicci kanka. Kana son a girmama ka amma ba ka girmama Ubangijinka, ga ka caba-caba cikin cabo, kazamar rayuwa na ba ka sha'awa, ka watsar da hankalinka, kai conka, kimtsa kanka tun ba ka makara ba.
   
  Allah Madaukakai Ya Ce: "Ba mu aiko manzanni face suna masu bushara, masu gargadi. To wanda ya yi Mani ya gyara, to ba tsoro a kansu kuma ba su bakin ciki. Wadannan da suka karyata ayoyinmu azaba na shafuwar su, saboda abin da suka kasance suna yi na fasikanci". An'am 48-49.


  Kuma Ya Ce: "Hakika ababen lura sun zo muku,to wanda ya lura don kansa kuma wanda ya makance, to kansa ya makance wa kuma ni ba mai tsaro ne a kanku ba. An'am 104.Kana ta karkata ga duniya da kokarin tara ta, tarawar wanda ya manta' "Ranar da dukiya ba ta amfani. Kuma diya ba su amfani. Sai wanda ya zo ma Allah da Iafiyayyar zuciya. "Shu'ara 88 - 89". Kana ganin haka na fissheka?

  Mun raba hudubar saboda yawansa,zamu ci gaba a kaso na 3


  isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb .Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Huduba daga Limamin babban Masallacin jihar Kebbi (kaso na 2) | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama