Najeriya ta baiwa mutum 335 'yan kasan waje 'yancin zama 'yan Najeriya

Gwamanatin tarayyar Najeriya ta baiwa mutum 335 takardar 'yancin zama 'yan Najeriya cikin su har da matar tsohon Gwamnan jihar Edo Lara Oshiomhole 'yar asalin kasar Cape verde.

Wannan ya biyo bayan kammala bincike da cika ka'idodi daga jami'an tsaron Najeriya wajen binciken wadanda abin ya shafa kafin a amince da zamansu 'yan Najeriya.

Ministan harkokin cikin gida Gen Abdulrahman Danbazau ya shaida wa manema labarai cewa mutum 500 ne suka mika takardar su ta neman zama 'yan Najeriya amma 335 suka cimma ka'idodin da ake bukata 245 kuma daga cikin su a bisa dalilin dadewa a Najeriya sai kuma 90 daga cikin su wanda sun zama 'yan Najeriya ne saboda sun auri 'yan Najeriya.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Najeriya ta baiwa mutum 335 'yan kasan waje 'yancin zama 'yan Najeriya Najeriya ta baiwa mutum 335 'yan kasan waje 'yancin zama 'yan Najeriya Reviewed by on May 16, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.