• Labaran yau

  Falasdinawa sun yi tattakin ranar Nekbe  Falasdinawa a Yammacin Gabar Kogin Jordan sun yi tattakin Nekbe na zagayowar shekaru 69 da takura musu gudun hijira wanda wata babbar musiba ce da ta taba samunsu.

  Dubunnan Flasdinawa ne suka yi tattakin a garin Ramalla na Yammacin Gabar Kogin Jordan.

  Mutanen sun yi tattaki daga dandalin Yessar Arafat zuwa na Al-Manara indsuka dinga daga tutuar kasarsu.

  A ranar 14 ga watan Mayun 1948 ne Israila ta mamaye kasar Falasdinu wanda ya tilasatawa Falasdinawa gudun hijira a ranar 15 ga watan na Mayu.

  Falasdinawa na kallon wannnan a matsayin wata babbar musiba da ta same su.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


   Falasdinawa sun yi tattakin ranar Nekbe ya fara bayyana a shafin TRT
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Falasdinawa sun yi tattakin ranar Nekbe Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama