Emmanuel Macron ya kama aiki a matsayin sabon shugaban Faransa

Sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha alwashin maido da kimar kasar a idon duniya, wadda ke fuskantar baranazar gushewa a baya....

Sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha alwashin maido da kimar kasar a idon duniya, wadda ke fuskantar baranazar gushewa a baya.
Macron mai shekaru 39, ya yi alkawarin ne a lokacin bikin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar ta Faransa, da ya gudana yau Lahadi a birnin Paris, sati guda bayan nasarar da yayi kan Marine Le Pen, a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu a ranar 7 ga watan da muke ciki, da kashi 65 na kuri’un da aka kada.Daga cikin manyan batutuwan da Macron yace gwamnatinsa zata fi bai wa muhimmanci akwai sabunta tsare tsaren tafiyar da fannin tsaron kasar, yin garambawul a fannin kwadago, sai kuma jagorantar sake saita ginshikan da suka kafa kungiyar tarayyar turai EU.

Macron da ya kuma yi alwashin daukaka ‘yancin Faransawa da dimokaradiyyar kasar, ya zama shugaban kasa mafi karancin Shekaru a tarihin kasar tun bayan Napoleon Bonoparte.

A gobe Litinin ake sa ran sabon shugaba Macron, ya bayyana sunan Firaministan da zasu yi aiki tare, kafin ziyara ta farko bayan rantsar da shi, da zai kai wa shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel a birnin Berlin.
Ana sa ran batutuwan da suka hada da, karfafa turakun da suka kafa kungiyar tarayyar turai EU, da kuma fannin tsaro su mamaye tattaunawar da shugabannin biyu zasu yi.

 
@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
 

Wannan labarin ya fara baiyana a shafin RFI

COMMENTS

Name

AL-AJABI,25,BIDIYO,1,BIRNIN-KEBBI,26,DUNIYA,23,FADAKARWA,23,FASAHA,3,HOTUNA,41,JAKAR MAGORI,20,LABARI,426,NISHADI,51,SANARWA,13,SHARHI,13,SIYASA,17,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Emmanuel Macron ya kama aiki a matsayin sabon shugaban Faransa
Emmanuel Macron ya kama aiki a matsayin sabon shugaban Faransa
https://3.bp.blogspot.com/-8tACguVMCZk/WRh7nvwnYwI/AAAAAAAAEnw/X-e1psbf-BgUlwXUFwhEofRN7gKtO8PKQCLcB/s400/fra.jpg
https://3.bp.blogspot.com/-8tACguVMCZk/WRh7nvwnYwI/AAAAAAAAEnw/X-e1psbf-BgUlwXUFwhEofRN7gKtO8PKQCLcB/s72-c/fra.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/05/emmanuel-macron-ya-kama-aiki-matsayin.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/05/emmanuel-macron-ya-kama-aiki-matsayin.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts KARANTA SAURAN LABARAI Karanta saura Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All KARANTA WADANNAN LABEL MAADANI BINCIKA GABADAYAN LABARAI Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy