• Labaran yau

  May 27, 2017

  Dan bautar kasa na NYSC ya mutu a jihar Kebbi | isyaku.com

  Wani dan bautar kasa na NYSC Yusuf Ege Olaide,mai lamba  KB/16 A/379, ya rasu ,shugaban hukumar kula da masu bautar kasa NYSC na jiha Alh.Lawal Turai ya shaida haka a yayin bikin rantsar da rukuni na A a sansanin horar da masu bautar kasa a Dakingari ranar Alhamis.


  Turawa ya yaba wa Gwamnatin jihar Kebbi bisa wakilai da ta tura Lagos garin mamacin da kudi N500,000 zaman gudunmawa saboda tafiyar da harkokin binne gawar.

  Ya kuma kara da cewa masu bautan kasa 2,200 ne aka watsa su zuwa cikin fadin jihar domin gudanar da ayyukan bautan kasa,ya kuma nuna gamsuwa da yadda matasan suka fahinci horon da aka yi masu.  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dan bautar kasa na NYSC ya mutu a jihar Kebbi | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama