"Buhari na a hannun kwararru a kasar Britaniya" | isyaku.com

Gwamnatin kasar Britaniya ta tabbatar wa al'umman Najeriya cewa shugaba Muhammadu Buhari yana a hannun kwararru a kasar ta Britaniya inda ake cigaba da duba lafiyarsa.

Wannan jawabin ya fito ne daga bakin Ministan sadarwa ta Najeriya Lai Muhammed a fadar shugaban kasa bayan kammala taron majalisar zartarwa a fadar ta shugaban kasa ranar Laraba.

Ministan ya shaida haka ne a yayin da yake amsa tambayoyi  daga manema labarai game da rashin lafiyar Shugaba Buhari.Ya kuma kara da cewa ba wani abin tsoro game da yanayin rashin lafiyar shugaba Buhari.

Shugaba Buhari ya fice Najeriya zuwa kasar Ingila ranar 7 ga watan Mayu inda ya sadu da Likitocinsa saboda ci gaba da duba lafiyarsa.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
"Buhari na a hannun kwararru a kasar Britaniya" | isyaku.com "Buhari na a hannun kwararru a kasar Britaniya" | isyaku.com Reviewed by on May 31, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.