Birnin Kebbi: Yadda hatsari ya rutsa da dan Acaba

Hatsari ya rutsa da wani bawan Allah dan acaba akan titin tsakanin magaman titin gidan Dr Bello zuwa randabawal na sabuwar kasuwa.

Babu wanda ya san makasudin aukuwan hatsarin,sautin bugun mota da dan acaban yayi daga bayan motan shi ya janyo hankalin jama inda nan take suka kawo agaji.

Ba'a san mai motar ba balle sunan dan acaban ko kuma daga ina ya fito,amma jam'a sun garzaya da shi da gaggawa zuwa asibiti.

Wani bawan Allah da yake wajen da abin ya faru mai suna Sani Shehu,ya bayyana wa ISYAKU.COM cewa hatsarin ya auku ne sakamakon ajiye motar da akayi kusan zakace akan hanya saboda ba'a ajiye motar a gefen titi kamar yadda ya kamata ba.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

 Kana da labari da kake son mu wallafa? ka gan wani lamari ya faru a gaban idonka da kake son Duniya ta sani? kana da ra'ayi ko shawara zuwa ga Gwamnatin jihar Kebbi ko na tarayya? ka aiko da lamarin ka zuwa birninkebbi080@gmail.com
Birnin Kebbi: Yadda hatsari ya rutsa da dan Acaba Birnin Kebbi: Yadda hatsari ya rutsa da dan Acaba Reviewed by on May 05, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.