• Labaran yau

  May 27, 2017

  Birnin kebbi: Yadda aka gudanar da bikin ranar Yara | isyaku.com

  An gudanar da bikin ranar yara a jihar Kebbi.Bikin wanda ya sami halartar mai girma Gwamnan jihar Kebbi amma daga bisani ya bar wajen taron saboda wani sha'anin aiki da ya taso da gaggawa.

  Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi Alh.Babale Umar shi ya ci gaba da wakiltar Gwamnan jihar Kebbi a wajen bikin.Daga bisani aka gudanar da rawar pareti wanda makarantun cikin garin Birnin kebbi suka gudanar.

  An gabatar da lakca akan illar shaye shaye ga rayuwar yara wanda kwamandan kula da masu sha da ma'amalla da miyagun kwayoyi na jihar Kebbi ya gabatar.

  Daga karshe an gabatar da kyautuka ga makarantun da suka ci na daya zuwa na uku.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Birnin kebbi: Yadda aka gudanar da bikin ranar Yara | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama