Birnin kebbi: Rigiman cikin gida na masu sayarwa da gyaran waya ya sa NSCDC ta yi sulhu

A 'yan kwanakin baya ne aka sami jita-jita a tsakanin kungiyar masu sayar da waya da gyaran waya na jihar Kebbi rigima da ya taso akan...

A 'yan kwanakin baya ne aka sami jita-jita a tsakanin kungiyar masu sayar da waya da gyaran waya na jihar Kebbi rigima da ya taso akan zargin makalewa akan mulki tun 2013 alhalin dokokin kundin tsarin mulki na kungiyar ya fayyace shekaru biyu ne kawai ga kowane shugaba.

Rashin gudanar da zabe ko samun wadataccen wakilci daga bangaren masu gyaran waya ya dade yana kawo tayar da jijiyoyin wuya tsakanin manbobin kungiyar inda wasu ke ganin Alh.Gimba wanda shine wanda ke rike da mukamin mataimaki bangaren masu gyaran waya amma ba'a taba ganin sa ba a rigima da ke shafan bangaren masu gyaran waya musamman idan lamarin ya kai ga jami'an tsaro.

Alh.Isyaku Garba zababben ciyaman na Olumbo Plaza wanda 'yan kasuwa masu shaguna a plazan suka zaba tun 2010 shine kuma mukaddashin ciyaman na masu gyara zalla wanda ke wakiltar duk wani mai gyara wadanda suka tsare gaskiya da mutunci a harkar sana'ar a Olumbo Plaza tun 2010.Alh.Isyaku ya bukaci masu da'awa da shugabanci akan cewa su iya banbancewa tsakanin iya hurumin kungiyar masu sayarwa da gyaran waya da kuma shugabancin Olumbo Plaza wanda aka kafa tun 2010 ita kuma kungiyar masu sayarwa da gyaran waya an kafata 2013 wanda shi Alh.Isyaku Garba shine ya kirkiro ta kuma ya rada mata suna HADTECH.

Shishshigi da babakere da ake zargin wasu mutane da yi a cikin lamarin tafiyar da Plaza ko kungiyar masu sayar da wayar ya janyo rashin fahinta da wasu mazauna Plazan ke ma kallon wuce makadi da rawa.Bincike ya nuna cewa wadannan mutanen har sun kai ga koran wasu yara masu sana'a akan laifin da za'a iya ladabtar da yaran ba sai an rabasu da hanyar neman abincin su ba wanda yinhakan ya tabbatar da rashin kwarewa a kan harkan ilimin hisabi da tasbihin adalci.

Daga baya bayan nan hatta yarinya mai sayar da shinkafa wasu mutane sun kore ta daga Plazan,amma sa baki da Alh.Isyaku Garba yayi ya kawo karshen takaddaman.

Bayan haka,lamura na ta tafiya a karkace a wani misali inda kanfanin wayar Tecno suka zo suka kafa wani katon posta ba tare da tuntuban jama'a da keda hakki akan hakan ba .Wani mai shago a plaza din da baya son a ambaci sunan sa yace ana zargin cewa kamfanin na Tecno ta tuntubi wani mutum game da lamarin amma shi kuma bai nemi amincewar masu shaguna ba sai kawai yace suje su sanya postan.

Daga karshe dai wani bangaren rigimar ya kai ga jami'an tsaro na NSCDC wanda bayan sauraron bangaren Alh.Isyaku Garba wanda ke da'awar cewa masu rike da mulki sun zarce ka'idar kundin tsarin mulki na kungiyar wanda ya tanadi shekaru biyu ga shugaba amma masu rike shugabancin sun makale tun 2013 zuwa 2017 da kuma bangaren Aliyu Tunga wanda suke jayayya da manufofin Alh.Isyaku.Bangarorin biyu sun sanya hannu a takardar yarjejeniya akan cewa za'a zauna lafiya.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Kana da labari da kake son mu wallafa? ka gan wani lamari ya faru a gaban idonka da kake son Duniya ta sani? kana da ra'ayi ko shawara zuwa ga Gwamnatin jihar Kebbi ko na tarayya? ka aiko da lamarin ka zuwa birninkebbi080@gmail.com COMMENTS

VISITOR
Name

AL-AJABI,22,BIRNIN-KEBBI,21,DUNIYA,19,FADAKARWA,22,FASAHA,3,HOTUNA,34,LABARI,351,NISHADI,49,SANARWA,13,SHARHI,8,SIYASA,15,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Birnin kebbi: Rigiman cikin gida na masu sayarwa da gyaran waya ya sa NSCDC ta yi sulhu
Birnin kebbi: Rigiman cikin gida na masu sayarwa da gyaran waya ya sa NSCDC ta yi sulhu
https://4.bp.blogspot.com/-BUCm2WrbTi0/WQ3U-knrnCI/AAAAAAAAEeU/QzBez8BR1r0iLfM07b6nTMCNFGjyel03wCLcB/s400/civil-defence.png
https://4.bp.blogspot.com/-BUCm2WrbTi0/WQ3U-knrnCI/AAAAAAAAEeU/QzBez8BR1r0iLfM07b6nTMCNFGjyel03wCLcB/s72-c/civil-defence.png
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/05/birnin-kebbi-rigiman-cikin-gida-na-masu.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/05/birnin-kebbi-rigiman-cikin-gida-na-masu.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All WASU KARIN LABARAI LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy