Bincike ya nuna cewa kashi 57 na 'yan Najeriya sun amince da Gwamnatin APC | isyaku.com

Wani rahoto da cibiyar tabbatar da kafuwar dimokradiyya a Nijeriya ta  fitar, ya nuna cewa kashi 57 cikin 100 na ‘yan Nijeriya sun gamsu da gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari.

Cibiyar, da sauran kungiyoyin kare muradun gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ne su ka fitar da wannan rahoto.

Rahoton ya ce,  kashi 57 cikin 100 da ke wakiltar mutane 4,097 a kananan hukumomi 111 da ke Nijeriya, sun yarda da cewa gwamnatin shugaba Buhari ta yi rawar gani a cikin shekaru biyu.

A bangaren  yaki da cin hanci da rashawa kuwa, kashi 52 cikin 100 sun amince da matakan da gwamnati ke dauka, amma kashi 47 cikin 100 ba su amince da matakan ba.@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com


Wannan labarin ya fara bayyana ashafi Liberty.
Bincike ya nuna cewa kashi 57 na 'yan Najeriya sun amince da Gwamnatin APC | isyaku.com Bincike ya nuna cewa kashi 57 na 'yan Najeriya sun amince da Gwamnatin APC | isyaku.com Reviewed by Isyaku Garba on May 30, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

Powered by Blogger.