May 11, 2017

Auren diyar IBB: 'Yan sanda 4000 zasu samar da tsaro lokacin bikin

Tsohon shugaban Nageriya a zamanin mulkin Soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida zai Aurar da diyar shi Halimat ga shahararren dan kasuwa kuma dan takarar mukamin Gwamna a jihar Gombe 2019 Alh.Auwal Lawal Abdullahi ranar Juma'a 12/5/2017.

Majiyar mu ya labarta mana cewa an kammala dukkannin tsare tsare da suka wajaba domin cima nassarar bikin Auren.Haka zalika Kwamishinan 'yan sanda na jihar Niger Zubairu Abdullahi ya ce an shirya samar da tsaro na sintirin 'yan sanda kimanin 4000 domin samar da tsaro a manyan hanyoyin cikin jihar da kuma filin saukan jiragen sama na Minna.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: Auren diyar IBB: 'Yan sanda 4000 zasu samar da tsaro lokacin bikin Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama