• Labaran yau

  May 20, 2017

  An sace kudin makamai akalla dala biliyan 15 a lokacin mulkin Jonathan a Najeriya

  Wani rahoto da aka fitar a Najeriya ya bayyana cewa, a tsakanin shekarun 2011 da 2015 an sace akalla kudin dala biliyan 15 da aka ware don sayen makamai a kasar.

  Rahoton  da Hukumar Transparency International da Wata Kungiyar Farar hula ta CISLAC suka fitar na cewa, sakamakon yadda farashin mai ya sauka a kaasuwannin duniya, barayin gwamnatin kasar suna amfani da bangaren tsaro wajen sace dukiyar kasa.

  Rahoton ya ce, tsaffin shugabannin sojin kasar sun sace dala biliyan 15 wanda ya kai rabin kudaden da ke asusun ajiyar Najeriya a bankin duniya.

  Rahoton ya kara da cewa, cin hanci da rashawa a bangaren aiyukan soji a Najeriya na yin barazana ga samar da tsaro tare da karfafa wa ‘yan ta’addar Boko Haram.

  Rahoton ya yaba wa gwamnatin Buhari da ke bincikar aiyukan cin hanci da rashawa a Najeriya musamman yadda ta tsare Sambo Dasuki, tsohon mai bayar da shawara kan sha’anin tsaro ga gwamnatin Jonathan da ta gabata.

  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


   An sace kudin makamai akalla dala biliyan 15 a lokacin mulkin Jonathan a Najeriya ya fara baiyana a shafin TRT


   
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An sace kudin makamai akalla dala biliyan 15 a lokacin mulkin Jonathan a Najeriya Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama