• Labaran yau

  An kashe mutane 8 a hari kan makarantar Islamiyya a Afganistan

  Mutane 8 ne suka mutu sakamakon harin bam da aka kai kan wata makarantar Islamiyya a jihar Pervan ta kasar Afganistan.
  Shugaban 'yan sandan Pervan Muhammad Zaman Mamuzay ya bayyana cewa, an saka bam din a karkashin kujerar da shugaban Shura na malaman Pervan Mevlevi abdul Rahim Hanafi ya ke zaune a kai.
  Mamuzay ya ce, bam din ya fashe a lokacin da ake tsaka ba wa daliban Hanafiyya karatu.
  Ya ce, daliban Hanafiyya 7 ne suka mutu inda wasu 6 suka jikkata sakamakon harin.
  Shugaban 'yan sandan ya ce, kungiyar ta'adda ta Taliban ce ta kai harin.
  Har yanzu babu wani da ya dauki alhakin kai harin.

  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb

   An kashe mutane 8 a hari kan makarantar Islamiyya a Afganistan ya fara bayyana a TRT

   
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kashe mutane 8 a hari kan makarantar Islamiyya a Afganistan Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama